Sojojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga fiye da 40 a Borno

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kashe ƴanbindiga fiye da 40 a wasu hare-haren haɗin giwwa ta sama a yankunan Azi da Musarram da ke jihar Borno.

Cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a a rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar a ranar Lahadi ya ce harin ya wargaza shirin ƴanbindigar na ƙaddamar da harin da suka shirya tare da bai wa sojojin ƙasa damar inganta ayyukansu a yankunan.

Ejodame ya ce rundunar ta kai hare-haren ne a ranakun 15 da 16 ga watan Janairun da muke ciki, bayan samun bayanan sirri da kuma haɗin kan dakarun sojin ƙasa da ke yankin.

Ya ƙara da cewa jirgin sojin saman ya kai ɗaukin gaggawa bayan da rundunar da samu rahoton cewa sojojin ƙasa na fafatawa da ƴanbindiga a yankin.

Ya ci gaba da cewa jirgin ya sake kai hari bayan da ya fahimci ƴanbindigar na sake taruwa a ƙarkashin wata bishiya a yankin, lamarin da ya haifar da kashe da dama cikinsu.

Sanarwar ta kuma ce kwana guda kafin nan jirgin yaƙin sojin saman ya kai wani hari kan wasu ƴanbindiga a gaɓar ruwar Tumbuns.

”Mun hango wasu jiragen ruwa 10 ɗauke da mayaƙa fiye da 40 na shirin kai hari garin Baga da madatsar kamun kifi, nan da nan aka kai musu hari tare da wargaza shirinsu”, in ji sanarwar

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda