Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 16, sun ceto mutum 11 da aka sace a Borno

Dakarun  Operation HADIN KAI sun kashe ’yan ta’adda 16 tare da ceto mutum 11 da aka sace a wasu hare-hare da suka kai a Jihar Borno.

Sojojin sun fafata da ’yan ta’addan a yankin Gidan Kaji da ke kan titin Maiduguri zuwa Damboa.

A yayin artabun, dakarun sun kashe ’yan ta’adda 16, yayin da wasu suka tsere da raunuka.

Sojojin sun kuma ƙwato kekuna sama da 20, makamai da sauran kayayyakin da ’yan ta’addan ke amfani da su.

A cikin wata sanarwa, Jami’in Yaɗa Labarai na Operation HADIN KAI, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce tun da farko sojojin sun daƙile wani hari da mayaƙan ISWAP suka kai sansanin soji da ke Auno a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2026.

Ya ce sojojin sun fatattaki maharan ta hanyar amfani da dabaru.

Ya ƙara da cewa a ranar 9 ga watan Fabrairu, sojojin tare da haɗin gwiwar Civilian Joint Task Force sun kai wani samame a yankin Komala da ke Ƙaramar Hukumar Konduga.

Sun bi sahun ’yan ta’addan har zuwa Gidan Kaji, inda suka kashe 16 daga cikinsu.

Laftanar Kanal Uba ya kuma ce sojojin sun kama wasu da ake zargi da kai wa ISWAP kayayyaki a yankin Bukarti.

A wani samame na daban da suka kai a ranar, sojojin sun daƙile yunkurin sace mutane a kan titin Buratai–Kamuya–Biu.

’Yan ta’addan sun bar waɗanda suka sace tare da tserewa zuwa cikin daji, bayan sun hango dakarun sojoji.

An ceto Mallam Idris Adamu da Mallam Muhammadu Safiyanu tare da miƙa su hannun iyalansu a Buratai.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda