Wakilan Arewa A Zauren Majalisa Sun Nuna Damuwarsu Kan Dokar Haraji
‘Yan Majalisar Wakilai da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya sun nuna damuwarsu kan wasu kudurori hudu da zasu sake fasalin dokar harajin Najeriya.
‘Yan Majalisar Wakilai da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya sun nuna damuwarsu kan wasu kudurori hudu da zasu sake fasalin dokar harajin Najeriya.
Gwamnatin Najeriya ƙarkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu na shan caccaka kan kama masu zanga-zangar tsadar rayuwa. Bayyanar faifan bidiyon wasu matasa da a ganin ido basu haura shekara 15 zuwa 20 cikin mummuna yanayi da aka kama sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa ya janyo wa gwamnatin Tinubu tofin Allah ya tsine a kafafen sada zumunta. Faifayin […]
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da shawarar Majalisar Tattalin Arziki (NEC) wadda ta nemi ya janye ƙudirinsa na ƙara haraji.
Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta ce za ta ɗauki mataki a kan jihohin da suka ƙi gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da ake sa ran zai tabbatar da cin gashin kai na ƙananan hukumomin kamar yadda kotun ƙolin ta zartar a kwanakin baya.
Bola Ahmed Tinubu ya wuce birnin Paris na ƙasar Faransa daga birnin Landan na Birtaniya a yau Juma’a.
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya naɗa shugabannin sabuwar Hukumar Raya yankin Arewa-maso-yammacin Najeriya. Bola Ahmad Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa sunayen shugabannin sabuwar Hukumar Raya Yankin Arewa-maso-yamma domin samun sahalewarsu. Wannan na zuwa ne bayan sanya hannu kan dokar da ta kafa hukumar da shugaban ƙasa ya yi a ranar 24 ga watan […]
Reno ya ce, da ‘yan Arewa ba su ga dama ba, da babu yadda Tinubu zai yi ya zama shugaban Najeriya.
Shugaba Tinubu ya yi kira ga matasa da su daina daga tutar kasar Rasha yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki a Najeriya.
Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta bai wa gwamnonin jihohin Najeriya 36, fiye da naira miliyan dubu dari 5 da 70 don tallafawa talakawa. Tinubu ya bayyana cewa suna aiko da sakon tallafi wanda suke saka rai zai isa ga al’umma. wannan na kunshe a cikin jawabin da shugaban ya yi […]
Magoya bayan shugaba Tinubu sun yi taro a Fadar Sarkin Kano da ke Nasarawa, gidan da sarki Aminu Ado ke zaune.