Makaho ne kawai zai ce Tinubu ya gaza ~Matawalle

Ƙaramin ministan tsaron ƙasar nan, Bello Matawalle, ya yi kakkausar suka ga masu ganin cewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya gaza.

Ya ce makaho ko kuma wanda ke da wata nufaƙa ne kawai zai ƙalubalanci irin nasarar da shugaban ƙasa ke samu a wannan lokaci.

Ƙaramin ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake martani ga batun da ke cewa akwai yuwuwar ‘yan Arewa ba za su zaɓi Tinubu ba a zaɓen 2027.

A ‘yan kwanakin baya-bayan nan ne dai, mai magana da yawun ƙungiyar Dattawan Arewa, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce ‘yan Arewa sun yi nadamar zaɓen shugaba Tinubu, inda ya ce daga yanzu yankin na Arewa zai fi mai da hankali ne ga haɗin kai wajen zaɓen shugaban ƙasa.

Sai dai ƙaramin ministan tsaron ƙasar nan ya ce sam wannan ƙungiya ba ta kai ta yi magana a madadin ‘yan Arewa gabakiɗaya ba.

Ya ce yana da tabbacin sauran shugabannin Arewa ba za su bari a jawo wa yankin abin kunya ba saboda kalaman ƙungiyar.

Post masu alaƙa

Babandede Ya Ziyarci Iyalan Hon. Laushi, Ya Ba Su Tallafi

Da Fulani Aka Kama da Wuraren ƙera Makamai a Filato, da War Haka Duniya ta Dauka:-Zagazola Makama

Gwamna Bala Mohammed ya canja sheka daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyyar APM