Shugaban ƙungiyar malaman jami’a, ASUU, farfesa Emmanuel Osodeke, Ya ce matuƙar gwamnatin tarayya ta gaza dakatar da yuwuwar cigaba da ƙaruwar kuɗin makaranta ba a jami’o’in ƙasar nan, akwai yuwuwar kaso 40 zuwa 50 na ɗalibai za su gaza cigaba da karatu daga nan zuwa shekaru biyu masu zuwa.
Shugaban ya yi faɗi hakan ne a yayin da yake gargadi game da makomar haɗin da ilimi ke ciki a yanzu a ƙasar nan.
Ya kuma zargi hukumomin jami’o’i da yunƙurin ƙarin kuɗin.
Shugaban ASUUn ya koka game da halin da iyaye za su samu kansu wajen cigaba da iya biya wa ‘ya’yansu kuɗin makaranta.
Inda ya ce har yanzu mafi ƙarancin albashin a ƙasar nan dubu talatin ne a wata, kuma a ciki mutum zai sayi abinci da biyan kudin sufuri da da sauransu.
Ya ce hatta iyaye da ke samun naira dubu hamsin a wata, idan aka ce kuɗin makaranta ya kai dubu ɗari uku, ta yaya za su iya biya wa ‘ya’yansu?
Domin haka ya yi gargaɗin cewa rashin ɗaukar mataki kan wannan al’amari zai sa ɗalibai da yawa su daina zuwa makaranta wanda kuma ƙaruwar matasa marasa ilimi a ƙasar ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
Har’ila yau, ya koka game da yadda gwamnatin tarayya ta ware kaso uku da ɗigo takwas ga fannin ilimi a kasafin kudin da aka yi na bana.
Inda ya ce kamata ya yi a ware kaso goma sha biyar cikin ɗari ga ilimin wanda hakan zai rage wa iyaye wahalhalun da za su iya fuskanta.
Game da batun rancen kuɗin karatu da gwamnatin tarayya ta ɓullo da shi kuwa, ya ce, wannan ba zai yi wa tasirin a zo a gani ba.
Kuma a maimakon rance, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta kira shi da tallafi.
Domin da yawa daga cikin ɗalibai ba za su iya samun rancen ba saboda cikin ƙa’idojin akwai cewa wajibi ne iyayen ɗalibin da zai nemi rancen ya kasance suna samun albashin da bai haura dubu ɗari biyar ba a shekara.
Inda ya ce iyaye nawa ne ke samun jimullar dubu ɗari biyar a shekra?
Domin haka, in ji shugaban wannan ba abu ne mai yuwuwa ba.