Home » Tartatsin Wutar Lantarki Ne Ya Haifar Da Tashin Gobara A Jami’ar Northwest Kano

Tartatsin Wutar Lantarki Ne Ya Haifar Da Tashin Gobara A Jami’ar Northwest Kano

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Jami’an hukumar kashe gobara reshen jihar Kano da kuma na gwamnatin tarayya sun samu nasarar shawo kan gobarar data tashi a jami’ar Northwest dake jihar .

Shugaban hukumar kashe gobara na jihar Kano, Sani Anas , ne ya tabbatar da hakan, lokacin da yake yi wa manema labarai karin haske kan musabbabin tashin gobarar.

Anas, ya ce ‘’sun hangi hayaki da misalin karfe 11 da minti 20am na safe daga ofishinsu, inda daya daga cikin jami’an su ya tabbatar da cewa gobara ce ta tashi a jaim’ar northwest.

Ya kara da cewa wutar ta tashi ne sakamakon tartatsin wutar lantarki, inda wutar ta lalata kayayyakin dake haw ana 9 da kuma taba wasu sassa a haw ana goma a ginin jami’ar.

Shugaban jami’ar Northwest, Farfesa Muktar Atiku Kurawa, ya ce jami’ar tana da tsari na kashe wutar lantarki duk lokacin da aka tashi da aiki, domin sun yi hutun salla babu dalibai a makaranta

Kurawa ya kara da cewa ba zuwa yanzu ba za su iya tantance girman asarar da suka yi, har sai jami’an hukumar sun tabbatar musu da cewa babu wata matsala sannan za su shiga don duba irin abubuwan da aka yi asara.

Ba a samu asarar rai ba, in banda mutum daya dake aiki a jami’ar da ya galabaita sakamakon shakar hayaki da yayi , har aka mika shi zuwa aisibiti don kula da lafiyarsa.

 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?