Tauraron dan kwallon kafa na kasar Ghana Asamoah Gyan ya sanar da rataye takalminsa.
A wani saƙon tuwita, Gyan ya ce “Lokaci ya yi da za a rataye riga da takalma yayin da na yi ritaya daga wasan kwallon kafa.”
Dan wasan na gaba ya ci kwallaye 51 a wasanni 109 da ya buga wa ƙasar, abin da ya sa ya zama dan wasan da ya fi cin kwallaye a tarihin Ghana.
Dan wasan mai shekaru 37, ya fara buga wasa a matakin ƙungiya ne a shekara ta 2003, inda ya buga wasa a kungiyar farko ta Ghana, Liberty Professionals, sannan ya buga wasa a Turai a Udinese ta Italiya da Rennes na Faransa da kuma Sunderland ta Premier ta Ingila.
Ya taba buga wasa a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a kungiyar Al Ain, ya kuma taimaka wa ƙungiyar ta lashe kofin babbar gasar ƙasar ta Pro-League sannan kuma ya zama dan wasan da ya fi cin kwallaye inda ya zura kwallaye 28 a wasanni 32.
A Ghana, Gyan ya yi fice a babbar tawagar kasar, Black Stars, a gasar cin kofin duniya ta Fifa guda uku – a 2006, 2010 da 2014.
Shi ne dan wasan da ya fi cin kwallaye a gasar cin kofin duniya a Afirka, inda ya ci kwallaye shida.
Ya buga wa ƙasarsa wasanni bakwai na gasar cin kofin nahiyar Afirka, inda Black Stars ta ƙare a matsayi na uku a shekara ta 2008 sannan a matsayi na biyu a 2010 da 2015.