Birtaniya ta sanar da cewa a shirye take ta rage haraji da take daurawa a kan kayayyakin da ake shigo da su daga Nigeriya da wasu kasashe masu tasowa.
Wata sanarwar da ofishin jakadancin Birtaniya dake Abuja ta fitar, ta bayyana cewa, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne da zummar farfado da ka’idojin cinikayya, da ceto sana’o’i da miliyoyin kudaden pounds da masu amfani da kayyayakin suke biya a kowace shekara.