Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi ganawar sirri da manyan hafsoshin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Villa.
Manyan hafsoshin sun isa fadar shugaban ƙasar da maraicen yau Talata, inda suka yi ganawa har ta tsawon sa’o’i uku, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.
Ba a dai bayyana dalilin ganawar ba, amma wasu na ganin ba ta rasa nasaba da matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Ganawar tasu na zuwa ne sa’o’i bayan Tinubu ya sanar da naɗin tsohon babban hafsan tsaron ƙasar, CG Musa a matsayin ministan tsaron ƙasar bayan saukar Badaru.
A cikin watan da ya gabata ne ƴanbidindiga suka sace wasu ɗalibai a makarantun jihohjin Kebbi da Neja, wani lamari da ya tayar da hankula a ƙasar.

