Majalisar Dattawa ta sanar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocinta, musamman na tsaro da na tattara bayanan sirri sakamakon ƙalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da ta fito daga kwamitin zaɓe na Majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
A sabon tsarin, Sanata Yahaya Abdullahi daga Jihar Kebbi ya zama shugaban kwamitin tsaro da na tattara bayanan sirri bayan ya bar kujerar kwamitin tsare-tsare na ƙasa.
An naɗa Sanata Shehu Buba daga Bauchi a matsayin shugaban kwamitin harkokin Kiwo, bayan cire shi daga kujerar kwamitin tsaro da tattara bayanan sirri makon da ya gabata.
Haka kuma, Sanata Mustafa Musa daga Yobe ya karɓi ragamar shugabancin kwamitin tsare-tsare na Kasa.
A bangaren kwamitin Sojin Sama kuma, Sanata Osita Ngwu daga Enugu wanda shi ne mataimakin shugaban Marasa Rinjaye a Majalisa ya zama muƙaddashin shugaban kwamitin bayan rashin lafiya ta hana tsohon shugaban ci gaba da aiki.
Majalisar ta ce waɗannan canje-canjen na da nufin ƙarfafa aikin sa ido da inganta martani kan batutuwan tsaro da ke tasowa a fadin ƙasa

