Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya isa Nairobi, babban birnin Kenya gabanin taron ƙoli na Afirka da Faransa da za a shafe yini biyu ana yi.
Shugaba Tinubu ya samu tarba daga jami’i a gwamnatin Kenya, Musalia Mudavadi wanda kuma shi ne sakataren da ke kula da harkokin da suka shafi ƙasashen ƙetare.
Akwai kuma Ministar harkokin waje ta Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu da Jakadan Kenya a Najeriya, Amb. Isaac Parashina.
Taron zai ƙara ƙarfafa ƙudirin Najeriya na zurfafa alaƙa da kuma haɗin kai da sauran ƙasashen Afirka da kuma Faransa.
