Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya rantsar da Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, mai ritaya a matsayin gwamnan riƙo na jihar Rivers, bayan ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihar, jiya Talata.
Bukin rantsuwar ya gudana ne yau Laraba a fadar shugaban Najeriyar da ke Abuja.
A ranar Talatar ne Tinubu ya sanar da sunan Ibas a matsayin wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar ta Rivers, bayan dokar ta-ɓaci da ya ƙaƙaba wa jihar, lamarin da ke nufin an dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa da kuma ƴanmajalisar dokokin jihar na tsawon wata shida.
- CP Ibrahim Bakori Yasha Alwashin Yaki Da Yan Daba Da Masu Kwacen Waya A Kano
- Cire Gwamna Fubara Ya Saɓa Wa Doka— Lauyoyi
Jihar Rivers ta kwashe tsawon lokaci cikin rikita-rikitar siyasa, lamarin da ya kai ga yunƙurin tsige gwamnan jihar da kuma rushe zauren majalisar dokokin jihar.