• Home  
  • Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 na naira tiriliyan 68
- Babban Labari

Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 na naira tiriliyan 68

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ƙasar na 2026 da yawansa ya kai naira tiriliyan 68.32. Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce cikin wannan adadi za a ware naira tiriliyan 15.8 domin biyan bashi. Kasafin ya kuma ware naira tiriliyan 15.4 domin ayyukan gudanarwar […]

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ƙasar na 2026 da yawansa ya kai naira tiriliyan 68.32.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce cikin wannan adadi za a ware naira tiriliyan 15.8 domin biyan bashi.

Kasafin ya kuma ware naira tiriliyan 15.4 domin ayyukan gudanarwar yau da kullum, yayin da aka ware naira tiriliyan 32.2 don gudanar manyan ayyuka.

“Yayin da kusan rabin kasafin zai tafi a manyan ayyuka, hakan na nuna burin gwamnati na ci gaba da ayyukan daidaita tattalin arziki ta hanyar bunƙasa ɓangaren tsaro da samar da ayyukan more rayuwa da ci gaban kowane fanni”, in ji sanarwar.

Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci hukumomin gwamnati su tabbatar da bin ƙa’ida da yin komai a bayyane da amfani da kuɗaɗen da aka ware musu ta hanyoyin da suka dace.

Haka kuma sanarwar ta ce shugaban na Najeriya ya ɗage fara aiwatar kasafin kuɗin ƙasar na 2025 zuwa 30 ga watan Yunin 2026.

Tun da farko an tsara fara aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 ɗin a ranar 31 ga watan Maris ɗin da muke ciki.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai