Tinubu ya tafi hutun mako uku

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai yi bankwana da Abuja domin tafiya ƙetare hutun makonni uku a matsayin wani ɓangare na hutunsa na shekara-shekara.

Sanarwar da Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce birnin Landan na ƙasar Birtaniya ne zai kasance wuri na farko da shugaban zai soma yada zango.

Sai dai Fadar Shugaban Ƙasar ta ce hutun na Tinubu zai kasance hutun aiki, inda zai ci gaba da gudanar da wasu ayyukan gwamnati yayin da yake ƙetare.

Ana sa ran shugaban zai dawo Najeriya bayan kammala hutun domin ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati da kuma shiga yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na watan Janairun 2027.

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai