• Home  
  • Tinubu ya yaba wa gwamnonin APC kan zaɓen fitar da gwani
- Babban Labari

Tinubu ya yaba wa gwamnonin APC kan zaɓen fitar da gwani

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana gamsuwarsa kan yadda ya ce gwamnonin ƙasar sun shirya tare da gudanar da zaɓukan fitar da gwani a faɗin jihohisu. Yayin da yake jawabi a mazaɓarsa ta Ikoyi bayan ya halarci zaɓen, Shugaba Tinubu ya ce ya ji daɗin yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana kamar yadda aka tsara. […]

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana gamsuwarsa kan yadda ya ce gwamnonin ƙasar sun shirya tare da gudanar da zaɓukan fitar da gwani a faɗin jihohisu.

Yayin da yake jawabi a mazaɓarsa ta Ikoyi bayan ya halarci zaɓen, Shugaba Tinubu ya ce ya ji daɗin yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana kamar yadda aka tsara.

”Wannan shi ne siyasa, siyasa ta tun daga tushe, inda kowane mambar jam’iyyarmu ke da damar shiga zaɓen kamar ni ma yadda na zo na yi”, in ji shi.

Shugaban Tinubu ya ƙara da cewa hakan ya nuna cewa Najeriya tana da tsarin dimokraɗiyya mai ƙarfi.

”Haƙiƙa na gamsu da yadda gwamnoni suka yi ƙoƙari a jihohinsu, wajen tarukan jam’iyyarmu tun daga matakin mazaɓa da ƙananan hukumomi da kuma zaɓukan fitar da gwani da tantance ƴantakara”, in ji shi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000