Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin 2026 a ranar Juma’a

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 a zaman haɗin gwiwa na Majalisar Tarayya a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 2 na rana.

Za a tsaurara tsaro a harabar majalisar, kuma duk waɗanda ke da aiki a majalisar dole ne su kasance a waje  aiki kafin ƙarfe 11 na safe.

An ƙiyasta kasafin kuɗin 2026 a kan Naira tiriliyan 54.4.

Hakazalika, Tinubu ya nemi Majalisar ta soke tare da sake tabbatar da kasafin kuɗin 2024 wanda ya kai Naira tiriliyan 43.56.

Manufar wannan mataki ita ce kada a yi aiki da kasafin kuɗi da yawa a lokaci guda, sannan a tabbatar da bin diddigin kashe kuɗi, musamman a ayyuka masu buƙatar kulawar gaggawa da tsaron ƙasa.

Rarraba kasafin kuɗin 2024 ya nuna Naira tiriliyan 1.74 don sauya doka, Naira tiriliyan 8.27 don biyan bashi, Naira tiriliyan 11.27 don kashe kuɗin yau da kullum wanda ba na bashi ba, da kuma Naira tiriliyan 22.28 don ayyukan ci gaba da gudunmawar asusun raya ƙasa.

An tsara wannan shiri ne don ƙarfafa tsari wajen kashe kuɗi da tabbatar da cewa kuɗaɗen ana amfani da su kamar yadda Majalisar ta amince.

Masana sun yi gargaɗin cewa tsawaita kasafin kuɗi na iya haifar da ruɗani, maimaitawa, da rashin tsara ayyuka yadda ya kamata, wanda zai iya shafar ci gaban tattalin arziƙi da kuma amincewar masu zuba jari.

Dokta Muda Yusuf, Shugaban Cibiyar Inganta Masana’antu (CPPE), ya ce, “Wannan hanya tana bai wa gwamnati damar sake tsara kasafin kuɗi.”

 

Ya ƙara da cewa, “Ci gaba na gaskiya zai buƙaci gyara gaba ɗaya maimakon gyare-gyare na lokaci-lokaci.

“Kasafin kuɗi dole ne ya dace da kuɗaɗen shiga na gaskiya kuma a fifita kashe kuɗi wanda ke tallafawa ci gaba.”

Masana sun ƙara da cewa yawaitar ciyo bashin gwamnati yana rage damar kashe wa sabbin ayyuka kuɗi.

Ingantaccen tsarin biyan bashi, in ji su, yana da muhimmanci wajen samun ƙarin kuɗi don ci gaba da tabbatar da cewa manufofin kasafin kuɗi sun cika.

Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Tarayya zai duba kuɗaɗen da aka gabatar kafin a amince da su gaba daya, kuma gwamnati na fatan wannan mataki zai samar da tsarin kashe kuɗi na gaskiya da kuma bin doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *