Majalisar dokoki ta jihar Kano ta tabbatar da mai shari’a Dije Aboki a matsayin cif joji ta jihar Kano.
Wannan naɗi nata ya biyo bayan aikewa da sunanta da gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi a cikin wata wasika ga majalisar dokokin jihar Kano wanda shugaban majalisar, Ismail Falgore, ya karanta ta a gaban majalisar a jiya.
Wannan ke nufi da kasancewar mai shari’a Dije Aboki a matsayin mace da ta zama cikakkiyar cif joji ta farko a tarihin jihar Kano.
Tun a baya dai, tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ayyana ta a matsayin mukaddashin cif joji a watan Maris ta jiha, sai dai a yanzu ta zama cikakkiyar cif jojin.