Tsananin zafin rana ya tilasta kwantar da alhazai fiye da 4,000 a asibitoci a saudiyya

Alhazai fiye da dubu hudu aka kwantar a asibiti sakamakon tsananin zafin rana a yayin aikin hajjin bana, cewar mai wani Magana da yawun ma’aikatar lafiya ta kasar a jiya laraba.

Dr. Muhammed Al-Abd Al-Aali ya kuma kara da cewa, yawan alhazan da suka fuskanci matsalar tsananin zafin ranar ya wuce dubu shida da dari bakwai.

Dr. Muhammad ya ce Sun shaidawa alhazai cewa kar su dauki kaya zuwa wurin jifa, da zuwa masallacin Ka’aba, sannan su kula da tafiya cikin natsuwa da kauce ma shiga turmutsitsi.

A ranar Arfa alhazai sun rika amfani da laima, yayin da zafin rana ya kai maki 45 a ma’aunin yanayi

Hukumomin Saudiyya dai sun samar da dubban ma’aikatan lafiya domin kula da alhazai a bana, yayin da masu aikin sa kai ke raba ruwan sha.

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro