Tsohon shugaban kasa, Buhari, ya sauya wurin zama saboda yawan jama’a masu kai masa ziyara

Tsohon shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya bar mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina inda ya tare tun  bayan saukarsa daga mulki.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da tsohon maitaimaka masa akan harkokin ƴaɗa labarai Malam  Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Sai dai malam Garba  shehu bai bayyana inda tsohon shugban ya komada zama ba.

Malam Garba Shehu ya ce, dattijon baya samun yadda yake so a garin na Daura, duk da ya bar kan mulki, mutane su na yawan kai masa ziyara, saboda haka ya sake lulawa zuwa wani wuri mai nisa domin ya yi rayuwa cikin sukuni.

Ya ce, Buhari ya koka da irin cinci-rindon da masu ziyara suke yi masa dare da rana a lokacin da yake kokarin samun hutu.

A cikin jawabin nasa malam Garba Shehu ya ce, dama  Buhari ya tafi Daura ne da nufin ya samu irin rayuwar da yake so ta rashin hayaniya, amma sai ya fahimci ba haka lamarin yake ba.

Post masu alaƙa

Manjo Janar Rabe Abubakar Ya Rasu A Hannun ‘Yan Bindiga

JIBWIS Gwallaga Sun Ziyarci A Sansanin Alhazai Na Jihar Bauchi Domin Bada Agaji

‘Yan Arewa A Jihohin Kudu Sun Koka kan Tsangwama da Wariya Saboda Matsalolin Tsaro