Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ko a jikinsa, game da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na ci gaba da binciken bidiyon dala da ake zargin an hasko gwamnan yana karbar rashawa.
Wannan na zuwa ne a lokacin da gwamnatin Kano ta bakin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Muhuyi Magaji Rimin Gado da aka mayar kan kujerarsa bayan gwamnatin Kano ta tube shi a baya, ya tabbatar da zai dawo da binciken da aka fara kan bidiyon gwamnan.
Baya ga bidiyon dala, akwai wasu zarge-zargen da ake yi wa gwamnatin ta Ganduje da ta gabata na yin wadaka da baitulmalin jihar musamman kudaden kananan hukumomi, da maganar kwangiloli da kudaden haraji.
Sai dai tsohon kwamishinan yaɗa labaran jihar Muhammad Garba, wanda na hannun daman tsohon gwamnan Kanon Abdullahi Ganduje ne, ya ce wannan abu ba ya daga masu hankali ko kadan.
A cewar Malam Muhammadu Garba ”wannan magana ce ta kotu, kuma shi Muhuyi a matsayinsa na lauya ya fi kowa sanin me ya kamata ya yi. Mun zuba ido mu ga abin da za su yi, idan yana da dama ya binciki maganar da ke kotu ya fi kowa sani, idan ma ba shi da dama ya fi kowa sani”.
A baya-bayan nan ne dai tsohon gwamnan Kanon ya nemi kotu, ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC daga duk wani bincike a kan lamarin bidiyon dalar, bisa hujjar cewa hukumar ba ta da damar gudanar da bincike kan lamarin ba.