Kasar Kamaru ta hana fitar da koko zuwa Najeriya, sakamakon kara da manoman koko a Kamaru su ka kai musamman a yakin kudu maso yammacin kasar.
Ministan Kasuwanci, Luc Magloire Mbarga Atangana, ya dauki matakin hana fitar da kokon zuwa Najeriya bayan wani taron rikicin da aka shirya a ranar 13 ga Yuni, 2023 a Yaoundé.
Tsawon shekaru da dama, masu gudanar da aikin noman koko a kasar suna zargin ‘yan Najeriya da fitar da kokon ta hanyar da ba ta dace ba musamman a yankin Kudu maso Yammacin kasar wanda ke iyaka da Najeriya.
Daga majiyoyin cikin gida a ma’aikatar kasuwanci, matakin da Ministan ya dauka ya biyo bayan ta’asar da ake tafkawa na fitar da danyen waken koko daga kasar zuwa Najeriya cikin ‘yan shekarun nan ta hanyar da bata dace ba.
Wannan lamari yana da matukar illa ga tattalin arzikin kasar Kamaru a cewar masana harkar kasuwanci da dama.