Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya shawarci, gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa sukar shirin N500bn na tallafin Shugaba Tinubu domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Hakan na ƙunshe ne dai a cikin wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ya fitar.
Sanarwar ta bukaci i, gwamnatin jihar Kano da jam’iyyar NNPP da su samar da ingantaccen shiri wanda zai rage raɗaɗin da mutanen jihar su ke ciki ba wai su riƙa neman abin aibatawa ba a shirin gwamnatin tarayya na rage raɗaɗin tallafin man fetur. Read
Idan za a iya tunawa, Gwamnatin jihar ta ce rabon tallafin ya fifita wasu jihohin akan wasu inda ya yi nuni da jihar Legas za ta samu kaso 47%, yankin Kudu maso Kudu zai samu kaso 17%, yayin da wasu yankunan za su samu kaso ɗan kaɗan.