Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce amfani da karfin soji kadai ba zai magance matsalar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ba
Ya bayyana haka ne ranar Lahadi yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai jihar Kano da ke arewacin kasar.
Yankin na Arewa maso Yammacin Nijeriya ya dade yana fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, wadanda kan bi mutane har gida ko su tare kan hanya, ko kuma su je makarantu su sace dalibai.
Gwamnatin kasar ta dauki matakai daban-daban domin magance matsalar, ciki har da yin ruwan bama-bamai da jiragen sojin sama kan maboyar ‘yan bindigar.
Sai dai duk da wadannan matakai, matsalar na ci gaba da ta’azzara musamman a jihohin Zamfara da Kaduna, inda ‘yan bindiga suka hana mutane sukuni.