• Home  
  • Yan Sanda Sun Mika Kwayar Tramadol Ta N150m Ga NDLEA A Kano
- Babban Labari - Labarai

Yan Sanda Sun Mika Kwayar Tramadol Ta N150m Ga NDLEA A Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta mika kwayar Tramadol ta naira miliyan 150 data kama ga hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar. Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis. Gwamna […]

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta mika kwayar Tramadol ta naira miliyan 150 data kama ga hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce tuni kwamishinan yan sandan jihar , CP Ibrahim Adamu Bakori,ya tabbatar da miƙa waɗanda ake zargin hannun NDLEA domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su gaban kotu.

SP Kiyawa ya kara da cewa an samu wadanda ake zargin da katon 6 na kwayar tramadol, kuma da aka kiyasta kudinsa ya kai naira miliyan 150, wanda tuni hukumar NDLEA ta yi amfani da na’urar gwaji inda ta tabbatar da cewar Tramadol ce.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000