Home » Wani Jirgin ƙasa ya yi taho mu gama da wata mota a jihar Ikko

Wani Jirgin ƙasa ya yi taho mu gama da wata mota a jihar Ikko

by Aishatu Sule
0 comment

Fasinjoji Da Dama Sun Jikkata a Wani Haɗarin Jirgin Ƙasa Da Mota a Jihar Legas. Wani jirgin ƙasa ya haɗu da wata motar fasinjoji a yankin Shogunle na Oshodi a jihar Legas.

Lamarin ya auku ne da safiyar yau Alhamis, inda shaidun gani da ido suka bayyana cewa motar tana ƙoƙarin wucewa ta kan taragon jirgin ƙasan ne lokacin da wani jirgi mai tahowa ya yi taho mu gama da ita.

Jirgin ƙasan ya yi tafiya mai nisa da motar inda tun daga Shogunle sai da ya kai ta yankin PWD a Ikeja. Fasinjoji da dama sun samu raunika a haɗarin da ya auku.

Wasu daga cikin shaidun gani da idon sun bayyana cewa motar tana ɗauke ne da ma’aikatan gwamnatin jihar Legas. Shaidun gani da idon sun tabbatar da cewa direban motar ya ƙi dakatawa ne a wajen tsayawa lokacin da aka tsayar da shi.

A cewar wani mai suna Babs wanda aka yi haɗarin a kan idonsa, ya ce lokacin da jami’an hukumar NRC suka dakatar da direban saboda jirgin da ke tahowa sai ya ƙi ya tsaya. Ya ɗauka cewa zai iya wucewa kafin jirgin ya ƙaraso.

Wani darekta a hukumar kiyaye haɗura ta jihar Legas, Adebayo Taofiq, ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa.

Shi ma Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa mutum biyu sun rasu a haɗarin.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?