Daliban jami’ar Bayero su 200 sun sami tallafin kudin makaranta da Sanatan Kano ta tsakiya sanata Rufa’i Sani Hanga ya biya musu.
Wannan na zuwa ne yayin da ɗalibai ke neman ɗauki daga gwamnati da masu hannu da shuni domin biyan kudin makaranta.
Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun nuna cewa, ‘yan majalisun tarayya na Bichi da Dambatta/Makoda da Wudil/Garko ne suke kan gaba wajen biya wa daliban yankinsu kudin makaranta bayan ƙarin kudin makaranta da jami’o’i suka yi.
Dalibai da dama na cikin fargabar gaza cigaba da karatun jami’a a sassan Kano bisa rashin kudin da za su biya kudin makarantunsu tun bayan karin kudin da aka yi.