DAGA: HASSAN ABDU MAI BULAWUS
Wasu dandazon mata sun gudanar da zanga-zangar lumana a kan gadar da ke ƙofar Nassarawa domin nuna goyon bayansu ga gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki a ɓangaren shari’a kan yin adalci a hukuncin zaɓen gwamnan Kano da ake dakon jiran ranar ƙarƙare shi bayan zaman farko da Kotun Kolin ƙasar nan ta yi.
Ga rahotan da Hassan Abdu Mai Bulawus ya haɗa mana kan wannan al’amari: