• Home  
  • Wata Kotu Ta Takaitawa Wani Tela Lokacin Yin Aiki A Kano
- Babban Labari - Labarai

Wata Kotu Ta Takaitawa Wani Tela Lokacin Yin Aiki A Kano

Wata kotu a jihar Kano ta samu wani tela da laifin gurɓata muhalli saboda karar da keken dinkin sa . Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar ce ta kai ƙarar telan mai suna Mubarak Yusuf, kan yadda keken ɗinkinsa da kuma injin janareto ke damun mutanen anguwar da yake da daddare. Wata sanarwa da ma’aikatar […]

Wata kotu a jihar Kano ta samu wani tela da laifin gurɓata muhalli saboda karar da keken dinkin sa .

Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar ce ta kai ƙarar telan mai suna Mubarak Yusuf, kan yadda keken ɗinkinsa da kuma injin janareto ke damun mutanen anguwar da yake da daddare.

Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce duk da cewa ya musanta zargin, amma ta gabatar da hujjoji da suka gamsar da kotun.

Har ila yau, kotun ta kai ziyarar gani da ido shagon da telan yake aiki, inda kuma ta tabbatar da cewa karar kekensa yana hana mutane bacci da daddare, abin da ya saɓa wa sashi na 7 na dokar kare lafiyar al’umma ta 2019.

“Don haka ne kotun ta yanke hukuncin taƙaita masa lokutan yin aiki, inda yanzu zai riƙa aiki daga karfe 6:00 na safe zuwa 9:00 na dare,” in ji sanarwar.

Kwamishinan muhalli na jihar ta Kano, Dakta Dahir Hashim ya yaba wa kotun bisa wannan hukunci, inda ya ƙara nanata zimmar ma’aikatar na ganin ta tabbatar da cewa kowanne mutum ko kuma wuraren kasuwanci sun bi matakan kare lafiyar al’ummar da kuma muhalli.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai