Rundunar yan sandan jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar mutane 5 yayin da wasu 10 suke samun kulawar likitotci a asibitin koyarwa na Mallam Aminu kano, biyo bayan tashin wani abun fashewa , a gidan Karfe dake kan titin Eastern Bypass.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa da safiyar ranar Asabar ya samu kiran waya daga baturen yan sandan Mariri, kan faruwar lamarin.
CP Adamu Bakaori , ya ce masu sana’ar gwangwan ne suka sako abubuwan a cikin mota daga jihar Yobe, kuma yanzu haka daya ne ya tashi yayin da sauran 7 jami’an tsaro ke yin kokarin katse su.
Tuni dai jami’an yan sanda suka rufe wajen tare da hana jama’a ketarawa.
Ya kara da cewa yawancin masu sanaa’ar gwanwan din suna tsintar tarkace dabam-daban, a bola da unguwanni, har suka tsinto abun suka saka a motarsu zuwa Kamfanin dake Kano.


