Home » Wata likita ta koka kan karancin zuwa duba lafiyar idanu a Najeriya

Wata likita ta koka kan karancin zuwa duba lafiyar idanu a Najeriya

by Anas Dansalma
0 comment
Wata likita ta koka kan karancin zuwa duba lafiyar idanu a Najeriya

A nan ma, Ƙungiyar Likitoci Musulmai ta Najeriya, IMAN, ta yi kiran ‘yan ƙasar nan da su riƙa duba lafiyar idanunsu a-kai-a-kai, domin yin hakan zai taimaka wajen magance ƙananun matsaloli ko cututtuka da kan shafi idanu.

Shugabar Mata ta wannan ƙungiya, dokta Maryam Ali, ce ta yi wannan kira a yayin ba da tallafi a jihar Jos na kwana ɗaya domin Ranar Idanu ta Duniya ta wannan shekera mai taken: “Kula da Idanu a Yayin Aiki”.

A cewarta, al’umma na da raunin fahimta game da kula da lafiyar idanunsu, inda ta buƙaci al’umma da su riƙa ziyartar asibitoci domin duba lafiyar idanunsu, ko da kuwa suna jin idanun nasu lafiya lau suke.

Ita ma wata ƙwararriya kan larurori da kan shafi idanu, dokta Fatima Umar, wacce aka yi amfani da wurinta aikinta wajen gudanar da shirin na kwana ɗaya, ta ce sanin muhimmancin idanu ne ya sa take duba mutane masu larurar gani, ba da gilashi da magunguna kyauta a wannan rana ta Idanu ta duniya.

Ta koka kan cewa mutane suna da ɗabi’ar cewa “ai garau nake gani”, inda ta ce a wani lokacin abin ba haka yake ba, domin har sai an duba za a iya tabbatar da hakan.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?