Home » An horas da lauyoyi kan shari’ar kasuwanci a Kano

An horas da lauyoyi kan shari’ar kasuwanci a Kano

by Anas Dansalma
0 comment
An horas da lauyoyi kan shari'ar kasuwanci a Kano

Ƙungiyar Lauyoyi Ɓangaren Shari’ar Kasuwanci ta gudanar da wani taro na shiyyar Arewa a nan Kano mai taken wanda aka yi da manufar inganta ayyukansu a ɓangaren haƙƙin mallaka da nazarin kasuwanci na duniya.

Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin na Ƙasa, Yakubu Chonoko Maikyau, wanda ya samu wakilcin dokta Adeoye Adefulu, ya ce sun kawo taron Kano ne saboda buƙatar da suka ga ake da ita na inganta ɓangaren sanin shari’ar kasuwanci domin samar da cigaban tattalin arziƙin jihar da ma maƙwabtanta.

Ita ma a nata ɓangaren, shugabar reshen Arewawacin Najeriya, dokta Fatima Kere-Ahmed ta ce sun shirya taron ne domin horas da lauyoyi game da faɗaɗa ayyukansu kan abin da ya shafi “haƙƙin mallaka da sauran kasuwanci.

Ta ce ƙungiyar an kafa ta ne musamman domin bunƙasa harkar shari’ar kasuwanci tare da wayar da kan al’umma game da muhimmancinta.

A nasa ɓangaren, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikata na fadar gwamnati, Shehu Wada Sagagi, ya ce yana da kyau lauyoyi masu tasowa da su shiga harkar shari’a da ta shafi kasuwanci domin bunƙasa tattalin arziƙi tare da kiransu da su dage wajen cin moriyar horaswar.

Haka ma, sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, wanda Walin Kano, Abba Mahe Bashir Wali ya wakilta, ya jaddada muhimmancin da ke akwai ga manyan ‘yan kasuwa wajen riƙo da hanyoyin shiga tsakani na shari’a wajen warware rikice-rikice domin tabbatar da zaman lafiya da kasuwanci a jihar nan.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?