Wata sabuwar doka ta sake fitowa a gasar kwallon kafa da za ce bakuwa kuma wadda ba taba ganinta ba.
Wannan sabuwar doka kuwa za ta karawa alkalan wasa karfin iko a kan kungiyoyin kwalkon kafan da suke yiwa alkalancin wasan domin kuwa sai abin da yaga dama zai yanke.
Sabuwar dokar ita ce dukkanin mai tsaron gidan da ya rike kwallo yana yanga ko jan lokaci ko kuma ya tsaya rangwada da gwalangwaso har ya dauki lokaci mai tsawo ba tare da ya buga kwallon cikin fili ba, to alkalin wasa zai baiwa abokiyar karawarsu kyautar bugun kusurwa (corner kick).
An fito da wannan sabuwar dokar ne sabo da mafiya yawan masu tsaron gida (goalkeepers sukan tsaya yin wannan abin wanda hakan yana sa wa a karar da lokaci musamman idan sun sami nasara.
Sai dai kuma ana ganin hakan zai iya sanyawa wasu alkalan wasan su musgunawa wasu kungiyoyin kwallon kafan.
Domin kuwa ko wanne alkalin wasa akwai kungiyar da ya tsana kuma sannan akwai kungiyar kwallon kafan da yake goyon baya ko da bai nuna a bayuane ba.