Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Amnesty International ta ce aƙalla fararen hula dubu 10 ne suka rasa ransu a hannun jami’an sojojin Najeriya, tun bayan ɓarkewar yaƙin Boko Haram a shiyar Arewa maso Gabashin ƙasar.
Amnesty International ta bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ta kira ranar Alhamis a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Yayin jawabinsa, Shugaban Amnesty a Najeriya Malam Isa Sunusi, ya ce a lokuta da dama jami’an sojojin Najeriya na ɗaukar duk wani da ya fito daga yankin da mayaƙan Boko Haram suke, tamkar ɗan ƙungiyar masu tada ƙayar baya ne.
“Sojojin Najeriya na ɗaukar duk wani wanda ke zaune ko kuma ya fito daga yankunan da Boko Haram su ke da iko da shi a matsayin mambar ƙungiyar.”
Isa Sunusi ya ce sun shigar da ƙara gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya da ke Hague, game da zargin cin zarafin ɗan adam da aka yi a shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ya ce muddin aka yi adalci ga rayukan da ba su ji ba su gani ba da mayaƙan Boko Haram da kuma sojoji suka salwantar, to ba shakka nan ba da jimawa ba za a kawo ƙarshen yaƙin Boko Haram.