Ya kamata a yi takatsantsan wajen ba wa Ganduje shugabancin APC ~ Dokta Salihu Lukman

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyar APC na ƙasa shiyyar arewa maso yamma  Dokta Salihu Lukman, ya ƙara jaddada cewa take-taken neman ɗora tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyar na ƙasa, ya saɓa wa dokokin jam’iyar ƙarara.

Haka kuma Dokta Lukman ya bayar da hujjojin cewa akwai fa maganar duba sanin ya kamata da ɗabi’u na gari kafin a ce za a naɗa Ganduje shugaban jam’iyar APC na ƙasa.

Dokta Lukman ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya nisanta kansa da duk wata ƙumbiya-ƙumbiyar neman naɗa Ganduje shugaban jam’iyar APC.

Post masu alaƙa

Babandede Ya Ziyarci Iyalan Hon. Laushi, Ya Ba Su Tallafi

Da Fulani Aka Kama da Wuraren ƙera Makamai a Filato, da War Haka Duniya ta Dauka:-Zagazola Makama

Gwamna Bala Mohammed ya canja sheka daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyyar APM