Da Fulani Aka Kama da Wuraren ƙera Makamai a Filato, da War Haka Duniya ta Dauka:-Zagazola Makama

Sanannen mai labarai da sharhi kan al’amuran tsaro a Najeriya Zagazola Makama ya ce, da Fulani aka kama da wuraren ƙera makamai a Filato, da war haka duniya ta ɗauki batun kamar wutar daji.

Zagazola ya ce, an ƙi kambama batun gano wuraren ƙera makamai a Filato ne saboda bai dace da abin da masu rura wutar rikicin ke yaɗawa ba.

Ya ce akwai waɗan da sun kwashi shekaru suna shirya ƙarya kan rikicin Filato, da masu neman yardar ƙasashen duniya da kuma wasu ‘yan siyasa da ke amfana da rikicin.

Ya ce” Mu ƙaddara Fulani aka kama da wuraren ƙera bindiga da sauran makamai, da war haka manyan kafafen yaɗa labarai sun ɗauka suna kiran kisan ƙare dang, da tuni a kafafen sada zumunta an ɗauki batun da zafi, da ‘yan majalisar Amurka fitar da bayani kan faruwar lamarin.

Zagazola ya ƙara da cewa da yanzu ”mata sun fito suna zanga-zanga tsirara, da matasa sun fantsama titunan Abuja, Amurka da Landan da sauran manyan birane da zanga-zanga saboda an samun Fulani da wurin ƙera makamai.

Ya ƙara sa cewa da duk harsashi ɗaya da aka samu a wurin ya zama shaidar cewa ana yi wa kiristocin Najeriya kisan ƙare dangi.

Zagazola Makama ya ce, shirun da aka yi abin tsoro ne, ya bayyana hakan ne a shafinsa na X.

Post masu alaƙa

Kano: Gini Ya Rufta Kan Mutane 16 Ciki Har Da Yara Shida

KACRAN: Babu wani babban rikicin manoma da makiyaya a Yobe

CP Ibrahim Bakori ya kai gaisuwar ban-girma ga Sarkin Karaye tare da halartar bikin rantsar da yan NYSC.