Daga: Safiyanu Haruna Kutama
Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kama wasu matasa biyu mace da Namiji da suka daurawa kansu aure a gidan cin abinci da shakatawa na Banana dake unguwar Zoo road a cikin birnin Kano.
Mataimakin kwamandan Hisba na Jihar Kano a bangaren kai sumame da ayyukan yau da kullum Dr Mujahideen Amenuddeen shine ya shaida hakan ga manema labarai a birnin Kano.
Yace bayan samun labarin daura auren a gidan cin abinci ba tare da waliyansu ba ,sai suka dana tarko domin kamasu ,saboda suna yawan zuwa wajen shakatawa bayan daura auren nasu.
- An Yi Zanga-zangar Kin Jinin Sabuwar Shugabar GGASS Tudun Bojuwa
- NLC Za Ta Fara Zanga-zanga Ranar 4 Ga Fabarairun 2025
Dr Mujahideen ya shaidawa kafar yada labarai ta VOA cewa sun kama ma’auratan ne a cikin daren ranar Laraba lokacin da sukaje wajen shakatawa.
Mataimakin kwamandan Hisbar yace abinda sukayi ya saba da shari’a kuma abin takaici ne, ace an daura aure babu ko daya daga wakilcin iyaye ko ‘yan uwa sai dai wakilcin abokai kawai wadanda ma duka kazo nazo ne.
A yanzu haka matasan mace da namijin suna hannun HISBA domin gudanar da bincike.