Daga Suraj Na’iya Idris Kududdufawa
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na ci gaba da cin karen ta babu babbaka a duniyar kwallon kafa a nahiyar Turai.
Hakan ya biyo baya ne dangane da yadda kungiyar ta Real Madrid ta zamo gagarabadau a kan dukkanin kungiyoyin kwallon kafan duniya musamman na nahiyar ta Turai.
A karshen makon nan da ya gabata kungiyar kwallon kafan ta Real Madrid ta fafata wasan hamayya na cikin gida na birnin Madrid (Madrid Derby) inda aka tashi kunnen doki 1 da 1 tsakanin ta da Atletico Madrid.
Biyo bayan kunnen dokin da ta fafata shine ya tabbatar da kungiyar ta ci gaba da cin karen ta babu babbaka sam ba a iya samun nasara a kanta har tsawon shekara guda a dukka in wata gasa sabo da dalilai kamar haka:
Ta fafata wasanni 40 a gasar Laliga ba tare da anyi nasara a kanta ba inda ta kwashe tsawon shekara.
Ta fafata wasanni 14 a gasar Zakarun Turai (Champions League) ba tare da anyi nasara a kanta ba.
Ta fafata wasannli 38 a filin wasanta na Santiago ba tare da an sami nasara a kanta ba.
Ta fafata wasanni 25 da ba a gidanta ba amma ba tayi rashin nasara ba.
Ta fafata wasanni 36 a dukkanin gasa a jere ba tare da an samu nasara a kanta ba.
Sannan kuma idan ba a manta ba Real Madrid ta lashe gasar Zakarun Turai na kakar wasan da ta gabata ba tare da tayi rashin nasara ba.
Sai dai kuma duk da wannan kokari da kungiyar ta Real Madrid ta keyi a haka magoya bayansu korafi sukeyi akan wani lokacin basa yimusu dai-dai.
Shin ko za a samu kungiyoyin kwallon kafan da za su kawo karshen Real Madrid a wannan sharafi da ta keyi a duniyar kwallon kafa?