Gwamnatin Jihar Borno ta ce za ta taikaita bikin zagayowar Ranar Samun ’Yancin Kai Najeriya na bana zuwa addu’o’i.
Wannan ya biyo bayan sakamakon mummunan ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri da kananan hukumomin da ke kewaye.
Kwamishinan Yada Labarai da Tsaro na jihar Borno, Farfesa Usman Tar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Farfesa Usman Tar ya jaddada bukatar zurfafa tunani tare da hadin kai a wannan lokaci na jarabawa a jihar.
Iftilain ambaliyar da aka fuskanta a Maiduguri ta shanye sama da kashi 70 na birnin Maiduguri kuma ta yi mummunar barna.
- An Buƙaci Matasa Su Ƙauracewa Zanga-zanga A Kano
- Ce-Ce ku-Ce ya Ɓarke Tsakanin Sojoji Da Jama’ar Kaduna
Rahotanni sun tabbatar da cewa ambaliyar ta shafi daruruwan iyalai tare da lalata muhimman ababen more rayuwa kamar asibitoci da makarantu da hanyoyi da gadoji.
Farfesa Usman Tar ya ambato Gwamna Babagana Zulum yana sake nuna tausayawarsa ga duk wadanda abin ya shafa tare da yin kira ga al’ummar Borno su hada kai wajen yi wa jihar da kasa baki daya addu’a.
“A yayin da ranar ’yancin kan kasarmu ya zagayo, dole ne mu mayar da hankali wajen tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta ranar 10 ga Satumba ta shafa.
“Mu yi amfani da wannan lokacin wajen yin addu’ar farfadowa da samun karfin gwiwa a jihar Borno da ma da Najeriya baki daya.
“Gwamnati za ta dukufa wajen gyara ababen more rayuwa da ambaliyar ta lalata da samar da agaji tare da tabbatar da cewa iyalan da abin ya shafa sun sami tallafin da ya dace,” in ji sanarwar.
Farfesa Babagana Umara Zulum ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na aiki da kwamitin rabon kudaden tallafi domin gaggauta isar kayan agajin da aka tara yadda ya kamata ga jama’ar jihar da iftilain ya shafa.