Ƙungiyar yan Kasuwar Kano (AKANOBCO) ta bayyana aniyarta ta haɗa gwiwa da rundunar ’yan sandan jihar wajen yaƙi da matsalolin shan miyagun ƙwayoyi, fataucinsu, ayyukan ’yan daba da sata a kasuwanni da sauran al’ummomi.
Kakakin Rundunar yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ƙungiyar ta bayyana wannan matsaya ne yayin ziyarar da shugabanninta suka kai wa kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano.
AKANOBCO, wadda ta ƙunshi ƙungiyoyin kasuwanni, ’yan kasuwa, masu kamfanoni da sauran masu gudanar da harkokin kasuwanci a jihar, ta yaba wa rundunar ’yan sandan bisa ƙoƙarin da take yi wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Amintattu na ƙungiyar, Alhaji Sabiu Bako, tare da Alhaji Tijjani Suleiman Garo, ta bayyana damuwarta kan yadda matsalolin shan miyagun ƙwayoyi, fataucinsu, aiyukan ’yan daba da sata ke zama barazana ga harkokin kasuwanci da zaman lafiyar al’umma.
Ƙungiyar ta nemi kafa ingantacciyar hanyar haɗin gwiwa da rundunar ’yan sanda domin inganta tsaro a kasuwanni, musayar bayanan sirri cikin gaggawa da kuma ƙarfafa aikin ’yan sanda na haɗin gwiwa da al’umma.
Haka kuma, ta buƙaci a riƙa wayar da kan ’yan kasuwa da sauran al’umma kan illolin shan miyagun ƙwayoyi, ayyukan daba da sata, tare da gudanar da tarurrukan tattaunawa akai-akai tsakanin shugabannin kasuwanni da jami’an tsaro.
Da yake mayar da martani, kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa shugabannin ƙungiyar bisa kishin ƙasa da jajircewarsu wajen neman zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin jihar.
CP Bakori ya tabbatar musu da cewa rundunar a shirye take ta haɗa kai da ƙungiyar domin tunkarar matsalolin tsaro, yana mai jaddada cewa tabbatar da tsaro ba aikin ’yan sanda kaɗai ba ne, illa nauyin da ya rataya a wuyan kowa.
Ya buƙaci shugabannin kasuwanni da ’yan kasuwa da su riƙa kai wa ’yan sanda sahihan bayanai kan lokaci domin taimakawa wajen dakile aikata laifuka, tare da nisantar shan miyagun ƙwayoyi, ayyukan daba da sauran laifuffuka.
Haka kuma, ya bayar da umarnin kafa tsarin tattaunawa da hulɗa na yau da kullum tsakanin rundunar ’yan sanda da ƙungiyar AKANOBCO domin tabbatar da dorewar haɗin gwiwar.

