‘Yan majalisar dattawan Arewacin Najeriya sun kalubalanci kudurin shugaba Tinubu

‘Yan majalisar dattawa na arewacin Nijeriya sun nuna adawarsu da yunkurin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, na yin amfani da karfin soji a kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.

Sun bayyana haka ne ranar Juma’a a yayin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rubuta wasika ga majalisar dattawan kasar yana neman amincewarta don daukar matakin soji kan dakarun da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a makon jiya.

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro