Ƴan majalisar tarayya sun amince wa shugaba Muhammadu Buhari, ya karɓo bashin dala miliyan $800m.
Mamban kwamitin kula da karɓo bashi a majaliaar wakilai, Abubakar Yunusa Ahmad ne ya bayya na hakan a jiya Jumu’a a hirarsa da manema labarai.
Ɗanmajalisar ya ce, sun kafa sharaɗin ba zasu bari gwamnatin Buhari mai barin gado ta kashe kuɗin baki ɗaya ba.
Haka kuma gwamnatin zababben shugaban ƙasa da ke dab da kama aiki tana da haƙƙin kawo na ta tsarin yadda bashin zai amfani ‘yan Najeriya.
Tun da farko, shugaba Buhari ya aike da takarda ga majalisar dattawa, yana neman su amince ya kara sunkuto bashin dala miliyan $800m daga bankin duniya.