Home » Yan Sanda Sun Fara Binciken Dalibin Jami’ar Da Binne Gawar Abokinsa Bayan Ya Kashe Shi.

Yan Sanda Sun Fara Binciken Dalibin Jami’ar Da Binne Gawar Abokinsa Bayan Ya Kashe Shi.

Wani ɗalibin Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya kashe abokinsa, wanda shi ma ɗalibi ne a jami’ar, sannan ya binne gawarsa a bayan gidansu.

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Wani ɗalibin Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya kashe abokinsa, wanda shi ma ɗalibi ne a jami’ar, sannan ya binne gawarsa a bayan gidansu.

Wanda aka kashe mai suna Peter Mafuyai, ɗalibi ne da ke shekara ta uku a sashen hada-hadar kuɗaɗen banki.

Ana zargin Nanpon Timnan da ke ajin shekara ta biyu daga sashen karatun harkar noma, da kashe shi sannan ya binne shi a rami.

Rahotanni sun bayyana cewar ɗaliban abokan juna ne sosai.

An ruwaito sun fita ƙwallon ƙafa, daga nan suka wuce wani waje sannan suka dawo gida.

“Da suka dawo Nanpon ya ɗauko adda. Abokansa da suke zaune tare a cikin gidan suka tambaye shi me zai yi da addar, sai ya ce yana son amfani da ita ne,” in ji wata majiya.

“Bayan haka sai ya sari abokinsa Peter da addar. Sauran abokan suka fara ihu suna tambayar dalilin da ya sa ya yi hakan, amma bai ba su amsa ba. Suka fita neman taimako, amma kafin su dawo, tuni ya binne gawar a bayan gidan.”

’Yan sanda sun riga sun gayyaci sauran abokan don yi musu tambayoyi, kuma ana ci gaba da bincike.

Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani kan dalilin da ya sa ya yi kisan, sai dai wata majiya ta ce wataƙila sun sama saɓani.

Sakamakon yajin aikin ASUU da ake yi a jami’ar, babu ɗalibai ya bare a samu cikakken bayani ba.

Da aka tuntuɓi Shugabar riƙon ƙwarya ta Sashen Watsa Labarai na jami’ar, Tongdyen Dachung, ta ce ba za ta iya yin magana kan lamarin ba tukunna, domin tana buƙatar tabbatar da wasu bayanai.

Ita kuwa Shugabar Ƙungiyar Ɗaliban Jami’ar (SUG), Jane Pwajok, ta ce lamarin yana hannun ’yan sanda.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?