Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta kai samame gidan tsohon Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle dake Gusau babban birnin jihar.
Rohotanni sun tabbatar da cewa an gano tare da kwashe motocin alfarma a yayin samamen a gidan tsohon Gwamnan dake rukunin gidajen alfarma na GRA a jiya juma’a.
har yanzu dai ba’a da tabbacin adadin motocin da aka gani a gidan, amma dai wata majiya ta tabbatar da an dauke motocin alfarma guda hudu a gidan
Kokarin jin tabakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ASP Yazid Abubakar yaci tura.
A kwanakin baya bayan nan Gwamn jihar Zamfara mai ci Dauda Lawal Dare ya zargi Matawalle da kashe tsabar kudi Naira Biliyan biyu da miliyan dari bakwai da casa’in da hudu da dubu Dari uku da talatin da bakwai wajen siyan motocin tawagar gwamna tare da yin awon gaba dasu bayan barin mulki.