Biyo bayan kara bunkasa aiyukan yan sanda a fadin Nijeriya, rundunar yan sandan jihar kano, ta samu gagarumar nasara cikin yan kwanaki kadan, kamar yadda babban sufeton yan sandan Nijeriya , Kayode Adeolu Egbetokun, ya bada umarnin kawo tsarin da za a yi amfani don magance aikata laifuka a fadin kasar.
Rundunar yan sandan jihar Kano, karkashin jagorancin kwamishinan ta, Ibrahim Adamu Bakori, wanda ya kama aiki a ranar 17 ga watan maris 2025, inda ya kawo tsare-tsaren tattara bayanan sirri da kuma aiyukan yau da kullum tare da bunkasa yadda ake aikin tsaro a Kano, domin magance abubuwan da suke damun al’umma.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce hanyoyin da aka bi an samu nasarar kama mutane 10 wadanda ake zargi da aikata laifukan, garkuwa da mutane da fashi da makami tare da samun kudi da makamai da sauran kayayyaki.
A ranar 18 ga watan maris 2025, da misalin karfe 11:00pm na dare, aka samu kiran gaggawa daga wajen wani matashi mazaunin unguwar Badawa, inda ya shaida wa yan sanda cewar yaga wadansu yan fashi da makami sun tsallaka gidan wani mutum a unguwarsu, inda aka tura jami’an yan sanda suka garzaya wajen har suka yi nasarar kama mutane biyu, da suka hada da Awwal Hassan Ibrahim da kuma Suleiman Umar dukkan yan asalin jihar Plato.
SP Kiaywa ya kara da cewa an samu bindiga kirar Beretta Pistol da kuma harsasi guda biyu.
- Yan Sanda Sun Kama Mata Cikin Wadanda Ake Zargi Da Yin Garkuwa Tare Da Karbar Kudin Fansa A Kano
- Isra’ila ta kaddamar da farmaki ta kasa a zirin Gaza
Haka zalika a ranar 18 ga watan maris 2025, an sake samun kiran daga wasu bayin Allah, inda suka tabbatarwa da yan sanda cewar sunga wata mota da suke zargin makamai ne a cikinta.
Bayan samun rahotan ne aka tura dakarun yan sanda tare da yin taratara aka kama wani matashi mai suna, Shu’aibu Yakubu wanda akafi sani da Dan Bula-bula mazaunin Kadawa Miltara, a lokacin da ake binciken motar an samu bindiga kirar AK47 da kuma harsasai guda 12.
Wanda ake zargin ya taabbatar da cewa basu da wani aiki da wuce fashi da makami a jihar Kano da birnin tarayya Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa a ranar 19 ga watan maris 2025, jami’ansu na RRT, sun kama wasu mutane biyu da suka hada da Friday Bitrus da Daniel Samuel dukkansu mazauna unguwar Zango Kano, dauke da bindiga kirar Pistol da harsasai guda 2 da kuma karamin Gatari da ake yin fashi dashi.
Rundunar ta kuma kama wasu mutane 5 da ake zarginsu da hada kai wajen yin garkuwa da wani matashi mai suna , Muhammad Bello dan shekaru 21, mazaunin garin Zakirai dake karamar hukumar Gabasawa Kano, inda masu garkuwa da mutanen suka nemi kudin fansar naira miliyan 15 kafin su sake shi.
Sanarwar ta ce tun bayan samun korafin ne kwamishinan yan sandan jihar Kano, ya tashi dakarun yan sanda karkashin jagorancin shugaban sashin dake yaki da masu garkuwa da mutane CSP Bala Shu’aibu, da su tabbatar da sun kubutar da matashin tare da kama wadanda suka aikata laifin.
Rundunar ta kara da cewa jami’an yan sandan sun yi amfani da sabbin dabarun aiki wanda kwamishinan yan sanda ya tsara har aka samu nasarar kubutar dashi tare da kama mutane 5.
Cikin wadanda rundunar ta kama sun hada da Tukur Lawan wanda akafi sani da Maikudi , Ado Usman da akafi sani da Ruwa , Sunusi Sirajo, Ummulkhairi Ibrahim da kuma Habiba Shu’aibu.
Binciken da yan sandan suka gudanar kan wadanda ake zargin an samu Bindiga guda 1 a wajensu da kuma kudin fansar da suka haka rami suka binne har naira miliyan hudu da dubu dari takwas da hamsin (N4,850,000:00) .
SP Kiyawa ya kara da cewa yanzu haka dai an dawo da su babban sashin gudanar da binciken manyan laifukan dake shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai don fadada bincike akansu kuma da Zarar an kammala gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu bakori, ya godewa jami’an yan sandan da suka yi wannan aikin tare da neman hadin kan al’umma a koda yaushe.