Ƴan sanda sun tarwatsa magoya bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, waɗanda suka raka ta zuwa Majalisar Dattawa daga babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda suka watsa musu barkonon tsohuwa domin kora su.
Magoya bayan sun yi tattaki ne domin raka sanatar zuwa majalisar domin ta koma bakin aikinta.
Tun da farko, majalisar ta buɗe ofishin sanatar da ke gefen Suite 2.05 a sashen Majalisar Dattawa.
Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta rubuta wa Majalisar Dattawa mako guda da ya wuce domin sanar da niyyarta ta komawa aiki bayan dakatarwa na tsawon wata shida, amma majalisar ta ce ta ɗan jira tukuna.
A watan Fabrairu ne dai tankiya ta ɓarke a zauren majalisar dattawa tsakanin shugaban majalisar, Godswill Akpabio da Sanata Natasha al’amarin dai ya kai ga har Akpabio ya umarci ɗaya daga cikin masu yi wa sandan majalisar hidima da ya fitar da ita daga zauren majalisar lamarin da ya kai ga dakatar da ita na tsawon wata shida.

