Daga Ali Rabiu Ali, Dutse
Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta samu nasarar kama wadanda ake zargi da satar Shanu da barayin Babura da kuma Dilolin kwaya.
Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Shisu Lawan Adamu , ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya manema labarai.
Rundunar ta ce ta kwato shanun sata guda uku da raguna guda Uku da baburan sata da tabar wiwi da sauran miyagun kwayoyi iri dabam-daban.
SP Lawan Shiisu Adam ya kara da cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani sumame da dakarun rundunar suka kai, a kananan hukumomin,Dutse, Kazaure, da kuma Ringim.
Mutanen da aka kama sun hada da, Jibrin Yahaya da wani mai suna Garba da Aliyu Abubakar, da kuma Musbahu Sabo da sauran su.
Kwamishinan yan sanda jihar, CP Dahiru Muhammad, ya yaba da kokarin jami’an da suka yi wannan kamen inda ya karfafa mu su gwiwa da su ci gaba da yin hakan don kakkabe aiyukan batagari a fadin jihar Jigawa.
