• Home  
  • ‘Yan Sandan Najeriya Sun Janye Gayyatar Sarki Muhammadu Sunusi II
- Babban Labari - Labarai

‘Yan Sandan Najeriya Sun Janye Gayyatar Sarki Muhammadu Sunusi II

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano na 16 Malam Muhammadu Sunusi II. 

KANO

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano na 16 Malam Muhammadu Sunusi II. 

Wannan na ƙushe a cikin wata sanarwar da Rundunar ta fitar da jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa ACP Olumuyiwa Adejobi ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce rundunar ta janye gayyatar ne biyo bayan shawarar da masu ruwa da tsaki suka basu da kuma gudun kar a yi wa aikin rundunar mummunar fahimta ko kuma a mayar da batun siyasa.

Maimakon sarkin ya je Abuja domin amsa tambayoyin rundunar, Sufeton ‘yan sanda na na ƙasa Kayode Egbetokun ya umarci ‘yan sandan da ke sashen tattara bayanan sirri su je Kano domin jin ta bakin Sarkin dangane da abin da ya faru a lokacin bukukuwan ƙaramar sallah.

Bayyanar wannan sanarwa ta janyo mabanbanta martani daga ‘yan Najeriya a kafafen sada zumunta.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000