Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano na 16 Malam Muhammadu Sunusi II.
Wannan na ƙushe a cikin wata sanarwar da Rundunar ta fitar da jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa ACP Olumuyiwa Adejobi ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce rundunar ta janye gayyatar ne biyo bayan shawarar da masu ruwa da tsaki suka basu da kuma gudun kar a yi wa aikin rundunar mummunar fahimta ko kuma a mayar da batun siyasa.
- Akwai Yuwuwar Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Shirin Yi Wa Kasa Hidima NYSC Shekaru 2
- Jihar Bauchi Ta Samu Tallafin Riga-kafin Cutar Folio Daga UNICEF
Maimakon sarkin ya je Abuja domin amsa tambayoyin rundunar, Sufeton ‘yan sanda na na ƙasa Kayode Egbetokun ya umarci ‘yan sandan da ke sashen tattara bayanan sirri su je Kano domin jin ta bakin Sarkin dangane da abin da ya faru a lokacin bukukuwan ƙaramar sallah.
Bayyanar wannan sanarwa ta janyo mabanbanta martani daga ‘yan Najeriya a kafafen sada zumunta.