Home » ‘Yan Ta’adda Sun Ƙone Coci Da Gidaje A Borno

‘Yan Ta’adda Sun Ƙone Coci Da Gidaje A Borno

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

‘Yan ta’addar ƙungiyar Boko Haram sun kai hari ƙauyen Shikarkir da ke Ƙaramar Hukumar Chibok, a Jihar Borno, inda suka ƙone wata coci da gidaje.

Wannan hari na zuwa ne kwana ɗaya, bayan wani hari da suka kai ƙauyen Bazir, inda suka kashe mutum biyu sannan aka ƙone wata coci.

A cikin wata sanarwa kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Daso, ya fitar, ya tabbatar da faruwar harin.

“Zaman lafiya ya dawo, kuma an ƙara tsaurarq tsaro. Muna tattara bayanai da kuma haɗa kai da sauran hukumomi domin tabbatar da tsaro da hana sake kai hare-hare.”

Wani mazaunin ƙauyen, Mallam Daniel Shikarkir, wanda gidansa ya ƙone, ya bayyana halin da ya shiga.

“Iyayena tsofaffi sun tsira ba tare da sun samu rauni ba, amma halin da muke ciki abun tsoro ne.

“Kwana ɗaya kafin wannan harin, maƙwabtanmu sun fuskanci irin wannan hare-hare, yanzu kuma ya zo kanmu.” kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?