Ƴan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun PDP, da NNPP, da kuma Leba, wato Atiku Abubakar, da Rabiu Musa Kwankwaso, da Peter Obi sun fara tattaunawa kan yiwuwar haɗewa da manufar kafa babbar jam’iyya ɗaya wadda za ta yi hamayya da jam’iyyar APC mai mulki.
Wata majiya ta ce, Kwankwaso da Atiku ne suka fara tattaunawa daga bisani suka shigar da Peter Obi.
Sai dai ba su tattauna wanda zai jagoranci jam’iyyar hamayyar da za su kafa ba, saboda suna jiran hukuncin da kotun sauraren ƙarar shugaban ƙasa za ta yanke.
Shugabannin jam’iyyun uku suna fata kotun za ta soke zaɓen Tinubu kuma ta sa a sake zaɓe.